20 Mayu 2015 - 18:34
An bada belin Sayyid Tahir Alhashimi

An bada belin wakilin cibiyar Ahlul-bait{a.s} ta duniya dake kasar Masar wanda jami’an tsaron kasar suka kama

Kamfanin dillancin labairai na Ahlul-Baiti{a.s}-abna-daya daga cikin fitattun ‘yan Shi’a na kasar Masar wanda aka kama ranar litini an bada belin shi yau.

Dokta Ahmad rasim wani fitaccan mutun a Masar yace, munyi kokari domin ganin mun samu belin shi kuma da yadar Allah hakarmu da cimma ruwa.

Ya kuma ce, kama Alhashimi na daya daga cikin sharrin da ake ma ‘yan Shi’a a kasar ta yadda ake tura mutane domin su kai ma ‘yan Shi’a hari yayin da yake zantawa da wakilin abna yace, cikin ikon Allah dokta Ahmad yak ore duk wata tuhuma da ‘yan salafiya kema Alhashimi wanda daga karshe ya karbo belin shi.ABNA